Video:- Malamar Coci Ta Karbi Musulunci

Shiriya ta Allah ce kuma yakan shirya wanda yaso ya kuma batar da wanda yaso, wannan baiwar Allahn ‘yar kimanin shekaru 51 data fito daga kasar Ireland me suna, Sinead O’Connor shahararriyar mawakiyace kuma ‘yar fim kuma malamace a wata cocin Katolika amma yanzu ta bayyana cewa ta karbi addinin musulunci.

Tayi fice sosai a zamaninta inda ta yi wakokin da aka saka su a fina-finai da dama kuma taci kyautar Billboard da ta MTV bila adadin haka kuma an sha saka wakokinta da sunanta cikin wanda za’a baiwa kyautar Grammy a lokuta da dama duk da dai bata taba lashewa ba.

A shekarar 2017 data gabata ta bayyana cewa ta canja sunanta zuwa Magda Davitt sannan kwatsam sai gashi yanzu tace ta bar addinin kiristanci ta koma addinin musulunci inda tace a lokacin da take malunta a coci duk wani littafi da zata karanta ta fahimci cewa yana karewa ne da tabbatar da gaskiyar addinin musulunci shiyasa ta fahimci cewa duk sauran addinai ba na gaskiya bane.

Ta bayyana cewa yanzu ta zabi sunan Shuhada Davitt.

Sannan kuma ta yi kiran sallah ta saka a shafinta na dandalin Youtube kamar haka:

Shuhada ta bayar da hakuri akan yanda bata fadi wasu kalaman kiran sallar da kyau ba, tace nan gaba idan ta koya sosai zata iya sosai kuma ta bayyana cewa wata abokiyarta ta kawo mata hijabi na farko ta saka.

Shiga Nan Domin Download Video Gaduje ya karbi Cin-Hanci, inji Ja-afar jaafar

Muna mata fatan Allah ya kara fahimtar da ita addini ya kuma karo mana irinta.

Download Video Now
Source www.PressHausa.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.