- Advertisement -

‘yar Wasan Hausa Fim Hauwa’u Maina Ta Rasu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

Innalillahi wa inna ilaihirrajiun. Allah ya yi wa Hauwa Maina rasuwa. A Yau 02-05-2018.

Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Hausa Hajiya Hauwa Maina ta rasu ranar Laraba da daddare.

Wani makusancinta ya shaidawa BBC cewa ta rasu ne a Kano bayan ta sha fama da jinya.

Ana sa ran za a yi jana’izarta ranar Alhamis a garin Kaduna, inda take zaune gabanin rasuwarta.

Hauwa Maina na daga cikin matan da suka jima suna fitowa a fina-finan Hausa.

Tun 1999 ta fara fim din Hausa, bayan ta koma garin Kaduna da zama.

Fim din ta na farko shi ne Tuba wanda Malam Yahya wani tsohon ma’aikacin gidan talabijin na kasa NTA ya bayar da umarni

Ta fara fitowa a matsayin budurwa, sai kuma matar aure, sannan ta koma tana fitowa a matsayin uwa.

A wata hira da ta yi da BBC Hausa da ba a kai ga wallafawa ba, Hauwa Maina ta ce ba kowane irin fim take amincewa ta fito ba.

ta ce tana fitowa ne kawai a fim din da ta gamsu cewa labarinsa ya yi ma’ana, kuma zai ilmantar.

Tuni dai jarumai na fina-finan Hausa suke ta bayyana alhini dangane da rasuwar jarumar, wacce da dama ke dauka a matsayin uwa.

Bayan fina-finan Kannywood, Hauwa Maina ta kuma fito a fina-finan Nollywood na kudancin Najeriya da ake yi da turanci.

Ita ce ta fito a fina-finai na tarihi kamar Quen Ameena sarauniyar Zazzau, da sarauniya

Daurama .

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

3 Comments
  1. YARIMA UMAR DAN JIGAWA says

    ALLAH UBAN GIJI YA JI KANTA YA KUMA GA FARTA MATA AMIN

  2. Salma Fagge says

    Allah akhbar Allah ygfrta mata ya sa aljanna ma koma Ameen

  3. Anas Habibu says

    Allah ya jikan hauwa maina Allah yasa ta huta….

Leave A Reply

Your email address will not be published.