Amfanin Gawai Ga Jikin Dan Adam Yaneda Yaww

Idan mutum ya samu zuwa wurin da ake gyara lafiyar jiki yana iya ganewa ashe, Actibated Charcoal anda ake kira (AC) ana amfani da shi wajen kara surar jiki. Wannan kuma ya jawo maganganu a kafafen sadarwa na Zamani. Shi Gawayi shekarun da suka wuce ana amfani da shi a matsayi na sinadari wajen hali na gaggaa, kamarsu guba, wajen amfani wajen cizon Kudin cizo, da sauran wasu raunuka wadanda suke ba masu girma ainun ba. Abin mamaki ne aji labarin cewar Millenials sun tsayar da shawarar amfani da gawayi domin maganin domin maganin asu cututtukan fata. Sai wannan lokaci ne aka gane yana da matukar amfani

Ba kamar gawayin da aka saba da shi ba wanda za, a iya samu da zarar an yi am fani da icce wajen girki, shi wannan Gawayin, ana samun shi wajen Kwakwa, da kuma dussar katako, abin da yasa suka bambanta tsaknin gaani icce da sauran shi ne, yadda ake dfadewa ana kona na ita ce zuwa wani lokaci mai tsawo, wannan kuma ya kansa ya kasance mai nagarta fiye da shi na Kwakwar.

Shi gawayin Kwakwa daban yake ana iya amfani da shi wajen kara kyau kamar dai Gawayi wanda aka saba da shi. Gawayin na Kwakwa idan an yi amfani da shi yana da wani sinadarin da ke fitowa da datti, idan aka shafa a fata, wannan maganin na gargajiya yana samar da wani abu mai tsotse duk wasu kwayoyin cuta, da kuma duk wasu abubuwan da ba, a bukata. Rage maiko maikon da ke fitowa daga jiki,

Bugu da kari shi wannan gawayi ana amfanin shi suna da yawa, bayan fitar da duk wani datrti a gashi, yana mayar da Hakora farare, duk asu abubuwan da basu dace ba, na kan fata suna lalacewa, ko akwai su ya kasance kamar babu, yana kuma sa fata ta kasancewa cikin haske da annuri.

Ganin yadda yake da inganci su masana hanyoyin gyara fata ta yi kyau sun bada shawarar ayi amfani dan kadan, don kada ya kasance da matsala a fatar mutum. Ko dai an yi amfani ne da sabulun AC , mai gyara fata, mai daukaka fuska, a tuna da amfani da Torner da zarar an yi amfani da shi.

Atiku Na Da Magoya Baya Da Yawa A Zariya –Bala

Tun bayan fice wa da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Abubakar Atiku ya yi daga jam’iyar APC ya kuma afka jam’iyar adawa ta PDP tagomashinsa a fage siyasa ya ke ta karuwa, wakilinmu Bello Hamza ya tattauna da wani matashin dan siyasa a yankin Zariya mai suna MALAM ABUBAKAR BALA in da ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa tafiyar Wazirin Adamawar ke kara haske, ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar ne kadai dan siyasar da ke da jajircewa da karfin gwuiwa da kuma kwar jinin da zai iya taka wa jam’iyar APC burki a kasar nan, ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya yadda Atiku Abubakar ya taka wa tsohon shugaban kasa burki a lokacin da nemi mugudra kudin tsarin mulki domin ya yi tazarce, ga dai yadda hirar ta mu ta kasance.

Za mu so ka gabatar mana da kan ka

Assalamu alaikum, suna na Abubakar Bala wanda ya ke manba ne a kugiyar Atiku Care Foundation na Samaru da ta ke karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna, ina kuma rike da mukamin Admin General ne na yankin Samaru.

Mene ne dalilin kafa wannan gidauniyar a Samarun Zariya?

Mun jawo wannan foundation din ne garin Samaru domin mu ma mu ci gajiya kyawawan aiyuka da manufofin kungiyar ne wadanda suka hada da taimakawa al’umma musamman mata da marayu da kananan yara wandada daman sune suka fi cancanta a taimaka masu a halin da ake ciki a na matsalolin tattalin arziki da gwamnatin APC ta jefa ‘yan Nijeriya a ciki, wannan gidauniya kuma ta na tallafawa dailiba masu karatu a mataki daban-daban, gaba daya burin gidauniyar ita ce bunkasa rayuwar al’ummar kasar nan.

Wadanne aiyuka Atiku Abubakar ya yi a yankin Zariya da ya sa ku a nan Zariya ku ke shaukin goyon bayansa?

Cikin aiyuka na baya-bayan nan da mai girma Atiku Abubakar ya ke gudanar wa a yankin Zariya shi ne gadan tsallake titi da ake ginawa a babban kofar shiga jamiar Ahmadu Bello, a halin yanzu aikin ya kai kusan kashi 90 na kamala wa, in an kamala aka kuma fara aiki da titin zai rage asarar rayuka da yawan hatsarin da ake yi musammam yayin da dalibai ke kokarin tsallake titi domin za su rinka amfani da gadan ne wajen tsallake, wa duk fadin Zariya babu irin wannan gadar, ko a haka mu ka tsaya, mu a yankin Zariya ya yi mana abin da babu wani dan siyasar ya yi mana tun da aka koma tsarin mulkin farar hula a ‘yan shekarun nan.

Wani canji ka ke ganin zai iya kawo wa ga halin da ake ciki na wahalar tattalin arzikin kasa in ya zama shugaban kasa?

Lallai kamar yadda ya ke fadi a wani bidiyo da aka wallafa in da yai bayanin naufofi da tsare-tsaren da zai wa kasar nan in ya zama shugaban kasa, yana bayanin irin alkawuran da wannan gwamnatin ta yi da kuma har yanzu ba ta iya cika ko da rabi ba, ya kuma bayyana matakai da tsare-tsare da zai gabata wanda za su bunkasa tattalain arzikin kasan nan cikin gaggawa, in kuma ka lura zaka gane cewa, Atiku babban dan kasuwa ne kuma kwararre a aikin gwamnati, saboda haka zai yi amfani da wannan kwarewar wajen samar da hurda da kasashen waje domin shigo da masu zuba jari a fannonin hakan ma’adanai, haka zai samar da aiyukan yi ga matasa abin da wannan gwamnatin ta kasa a cikin kusan shekara 3 da ta ke mulki.

Atiku Abubakar kuma kwararren dan siyasa ne da zai iya hada kan kasar nan, musammam a wannan lokacin da wasu bangare ke kiraye-kiyaren raba kasa. A harkar tsaro kuma wannan gwamnatin ta kasa tsayar da zub da jinin ‘yan kasa, kullum sai kaji labarin a kashe a wannan bangaren ko waccan, Alhaji Atiku zai yi amfani da kwarewarsa wajen dakile rikice-rikicen da ke faruwa, Tabbas mu a shirye muke mu goya wa Atiku baya a ko a wanne jam’iya ya fito takarar shugabancin kasar nan.

To wani kira za ka yi ga matasa ‘yan uwanka da kuma sauran ‘yan siyasa na su shigo jirgin Atiku domin a tsira tare?

Gaskiya ina kira ga musamman ainihin wadanda suka fito daga jam’iyar PDP tun da a halin yanzu a nan ne Alhaji ya koma da su hada kan su domin fitar da ‘yan takarar da suka dace musammam a bangaren takarar gwamnan a jihar Kaduna a tabbatar da an tsayar da Alhaji Sani Bello, Mainan Zazzau a kuma zaben shugaban kasa, a tabbatar da Alhaj Atiku Abubakar ne aka ba tutar takarar shugabancin kasar nan domin shi ne kadai ya ke da karfi da kwar jinin da zai iya fuskantar duk wa ta barazana da jam’iyar APC za ta iya yi a fagen zabe a kakar zabe mai zuwa. Ka da mu yarda da yaudarar da aka yi mana a shekarun baya, kowa ya iya allosa ya wanke.

Anya Da Hakan Za A Yi Jagorancin?

Daga Idris Aliyu Daudawa

Sau da yawa ma wasu al’amuran suna bani mamaki to mamaki mana saboda mai dokar barci ne amma sai kaga ga shi yana ta gyangyadi, abin da ya kasance ke nan ba cinya ba kafar baya, sai ta kasance abin da yak e fadi daban wanda kuma yake aikatwa daban. Kamata ya yi shi mutum ko wane lokaci a same shi kaifi daya kar ya kasance, yana da harshen Damo, ko kuma ya fadi magana yanzu dan an dan jima kuma idan yaga idon wani sai ya canza. Shugabanci nagari koda yaushe shi yafi dacewa kada mutum ya kasance Indararo wanda koda yaushe a cikin bari yake, ba kuma yaba gida shi sai daji. Ko yaushe ana girma ne amma kuma ana asa da kasa, wasan ma da ‘Yan yara, a irin wannan haliai zai wuya a samu wata doguwar tafiya,ba yaba gida sai daji, shi yana son wai gidan shi ya ci gaba akan hanya madaidaiciya, amma kuma da ya samu baradwa yake yi, ya kasance Tifa wadda ita ko da irin tafiyar da ba , a samun ko ‘yan rakiya saboda ai yanzu mutum ake kiwon an daina kiwon dabbobi, duk wasu abubuwan da mutum yake akwai masu lura da shi, idan shi yana tsammanin babu mai ganin shi.

Don haka wani lokaci ma har sai ma abin ya daurewa mutum kai idan ya ji yadda mutane ke saurin yanke hukunci akan wani, kamar dama jira suke a yi magana akan shi. Ana cewar ai ga wane shi ya kamata ya yi abin ko kuma harkan jagoranci, nan take zasu nun rashin amincewarsu, suna cewa idan dai wane ne to sai dai, a fasa yin koma mene ne.

Ba yadda mutum zai yi zamanin shi ya kuma ce zai yi na wani ko wasu ba, komai da lokacinsa, da wuya kuma idan lokaci ya wuce ace ya sake dawo, shi yasa da zarar an samu dama ake amfani da ita saboda da zarar ta bare ko wuce to bafa ta kara dawowa. Ko wane lokaci kar mutum ya dubi kan shi, kamata yai ya dubi baya ya gani, matuka ya riga nuna shi ko da yaushe shi ne zai wuce gaba, domin in shi ne yau, ba shi ne gobe ba, idan ba mutuwa to akwai wata lalura ta halin rayuwa, wadda ba wanda ya san yadda ta kasance. Ba wai ana fata bane ba amma ba wanda ya san gobe sai Allah, domin shi ke da komai.

Maimakon ace zuwa yanzu an yi nisa wajen dasa matasa wajen koya masu makamar al’amura da kuma gwada su, wajen fara nuna masu makamar al’amura, idan sunyi kuskure sai a gyara masu, gobe ba zasu sake maimaita hakan ba, sai ma a fara gogewa. Yanzu ga shi lokaci na tafiya sauran sassa basu bakinciki da abin da nasu zasu samu, to ku abin naku ba haka yake ba, koda yake ba, ku kallon ne zaku iya samu ba, watarana ba wai zaku iya ganin alherin da zai kasance a shi wannan sashen naku ba.

Haba kuke nan dai kullun baku damu da yadda sashen naku yake ba, ku dai kullun ku taba ku ji aljihunku yayi ninkis da abokanen rayuwa, ai ba, a girma sannan kuma ace za, a ci gaba da yin wasa da kasa. To wasa kasa mana, ta wani fannin ma ai gara ma wasa da kasa irin wanda ‘yan yara suke yi, dominsu an san lokaci ne da akwai ranar da zasu bari. Idan ma kace masu kasan lokacin da suka yi wasan sai suce ai ba haka bane, ku kuwa da ku Kakannin sune amma kuma halin naku ya kasance kuna nuna kamar ba kusan inda yake maku ciwo ba.

Lokaci fa wucewa yake kullun kuma sababbin al’amura na shigowa, idan kuma baku yi yanzu ba, to kuma har yaushe zaku yi, kada fa har a kai ga bari ruwa ya kare wad an kada bai gama wanka ba. Akwai fa ranar da za ta kasance baku nan, ko kuma kuna nan tana iya kasancewa ba zaku ioya yin wani abu ba, wanda har za , a saurareku. Kamata ya yi ku tanaji magani kafin ciwo ya zo, kamar dai yadda wasu suke yi. Ba sai abin ya zo ba a fara yin wasu ‘yan kame kamen da tsugunni tashin da ba zasu yi wani amfani ba. Waje daya kuma sauran wuraren sun wuce gabasun yi ma naku fintinkau, sun yi dogon tashi irin na jirgin sama, amma mu kuma naku bangaren gasu can wani lokaci ma, mashi ma ba mota suna fuskantar, gwada ko zasu iya dan tabukawa su gani. Lokaci fa ya yi yanzu wanda duk Tsuntsu idan har ya amsa sunanshi na to ya rika yin kukan gidansu, bai kamata ko ma kwaikwayon na wasu ya rika yi ba, idan ana tafiya, ana duba baya sai a tuna da akwai wadanda ya dace, a sasu gaba a tafiyar saboda suna da rauni , ba kuma zasu iya ba su kadai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.