Hausa News:- Rahama Sadau Tace Ita Ba Budurwa Bace Domin Tasan Dadin Na Miji

Ranar Asabar data gaba ta ne wani abun mamaki ya faru a inda jaruma Rahama Sadau ta yi alkawarin amsa tambayoyin masoyan ta a shafin ta na Instagram da aka mata cikin mintuna talatin na farko.

Daga cikin tambayoyin, sai ko wani ya tambaye ta ko ita budurwa ce wato ko bata taba sanin namiji ba, abun mamakin sai jarumar ta cika alkawarin ta a inda ta fada masa gaskiya cewa ita ba budurwa duk da yake kowa ya san bata taba aure ba.

Da alama jarumar na ganin ba wani abu ba ne don mace ta rasa budurcin ta kafin tayi aure, tunda ita ba yarinya karama ba ce;laifin ta kawai shine fadin gaskiya.


Da alamu jarumar tayi nadamar wannan fadin gaskiyar, domin korafe-korafen mutane yasa ta goge ‘post’ din, Amma aikin gama ya gama.

Yanzu muhawara ta rage wa masu saurare: Kuna Ganin laifin Rahama Sadau da ta bayyana hakikanin “virginity status” din ta?

Kuna Ganin wannan Amsa Tayi Daidai???

©Arewa24

Leave A Reply

Your email address will not be published.