Sakon Rabi’u Biyora Zuwaga Makaraban Manyan Buhari


Duk Wanda baisan mene Dalilin da yasa Rabiu Biyora ya dena rubutu domin Kare gwamnatin Baba Buhari ba to ya karanta wannan Sakon Nashi….👇🏻👇🏻👇🏻
Rabi’u Biyora ya fara da cewa;

“Wallahi tallahi bawai saboda bukatar kaina ni kadai ba, nake dagewa akan lallai sai an samu gyara ba, halayyar da ake nunawa matasan Arewa masu kare Gwamnatin Baba Buhari lamarin ba dadi ko kadan, shiisa na zabi wannan hanyar nake gudanar da yajin aikin kare ayyukan Gwamnatin, ko hakan zai temaka a samu sauyi, babban burina inga matasa suna amfana da siyasa, tunda suma manyan ba kyauta suke ba.

Yanzu ace duk matasan dake kare baba Buhari ba wanda ya iya samun aikinyi albarkacin soyayyarsa ga Gwamnatin duk da cewa dayawan matasa sun gama karatu, akwai bukatar a samu gyara, idan basu gyara ba sai a saka musu idanu su tafiyar da Gwamnatin su kadai….

Bamu da matsala da baba Buhari tunda ya sauke hakkin bayar da mukamai ga mutane masu yawa, kenan sune ya kamata ace suna shigewa gaba wajen nemawa matasan arewa abun alheri, ba ina magana bane akan PA kawai bane na baba, ina SA suke ina ministoci suke ko ana nufin ace basu san aikin da matasan keyi bane, ko kuwa sun dauka su kadai ne keda bukata amma sautan matasa basu da kowacce bukata a duniya sai yin aiki zallah..

Ya kamata mu dinga gayawa kammu gaskiya”

Kar Mutane Su zamo Masu Magana akan rashin Sanin abun dake faruwa….. Kar kiyayya da rashin Sanin ciwon kai ya hanamu fahimtar Gaskiya a matsayinta na Gaskiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.