Budadiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Shugaban Kasa Muhammad Buhari

Assalamu Alaikum.
Maigirma shugaban kasa ni masoyinka Datti Assalafiy na yanke shawaran rubuta wannan budaddiyar wasika domin na ankarar da kai cewa kana dab da rasa wasu manyan masoyanka da suka sadaukar da komai nasu suke maka hidima a duniyar social media

A kwanakin baya nayi amfani da wannan damar na ankarar da mukarrabanka domin suyi abinda ya dace kar rasa masu yiwa gwamnatinka hidima a social media, to amma daga baya sai na fahimci cewa su ma abin ya fi karfinsu, wannan dalilin ne yasa na yanke shawaran rubuta maka wannan budaddiyar wasika

Maigirma shugaban kasa akwai wasu bayin Allah musamman a wannan dandali na facebook da suke maka hidima shekara da shekaru ba tare da sun samu tallafi daga wajen kowa ba, sun sadaukar da dukiyarsu da lokacinsu har ma da rayuwarsu wajen yi maka hidima ba dare ba rana, suna da miliyon mutane da suke wayar musu da kai akan kyawawan manufofinka, suna da engagement a facebook wanda yawansu ya kai sama da miliyon ashirin wallahi, suna da kamfanonin yada labarai da suke amfani da su wajen yi maka hidima, aikin da suke ya fi na wasu daga cikin manyan mukarrabanka da ka basu amana, amma har zuwa yau basu taba samun tallafi daga gurinka ko wakilinka ba..

Akwai wasu bayin Allah da a yanzu haka sunyi amfani da dunbin dukiya suka gewaya kusan fadin tarayyar Nigeria suna tattara bayanai na ayyukan alheri da kakeyi, suka tattara muhimman abubuwa naka wanda ko jami’anka ba kowa ya san da haka ba, suka shirya wani gagarumin video zasu watsa a duniya ta dukkan manhajar kafofin watsa labarai da ake dasu, amma saboda anyi watsi da su sun dakatar da abin, kuma yanzu haka suna shirye-shiryen tafiya yajin aiki na kin tallataka a social media, zasu dakata daga yimaka hidima tunda anyi watsi da su

A yanzu haka akwai manyan jiga-jigan ‘yan social media da suka fara komawa bangaren Atiku Abubakar, Maigirma shugaban kasa idan baka dauki matakain da ya dace ba to za’a fuskanci babban kakubale da cikas ta hanyoyi da dama a tafiyarka, abune da na bincike shiyasa nake ankarar da kai

Wadannan masoya na ka ‘yan arewa da suke maka hidima a social media da akayi watsi da su; suna ta korafin cewa ‘yan uwansu ‘yan kudanci musamman yarbawa anfi kulawa da su, misali; kwanaki matasan yarbawa sun kai korafinsu suna da kananun kamfanoni na watsa labarai da kungiyoyinsu da suke aikin tallata Buhari a yankin yarbawa don haka suka bukaci da a basu taimako, muna da masaniyar cewa an basu tallafi na miliyoyin naira

Sannan ga misali da abinda akayi jiya a Lagos, an dauki matasan yarbawa aka musu lakabi da cewa sojojin Buhari ne wanda yawansu ya kai mutum dubu biyar, Baba Tunde Fashola ya jagoranci mutanen, a cikinsu akwai ‘yan social media, akwai ma’aikatan gidan rediyo da talabijin masu zaman kansu, aikin da zasuyi shine su kare Buhari a yankin yarbawa, kuma gaba dayansu an musu alkwari da yarjejeniya za’a biyasu albashi mai tsoka saboda zasu tallata Maigirma shugaba Buhari

Bai wuce wata daya ba, Bola Ahmed Tinubu yaje Lagos ya sa aka tara mishi matasa da zasu tallata Buhari a social media, yace su fadi dukkan bukatunsu za’a biya musu, Maigirma shugaban kasa Buhari idan har za’a nunawa yarbawa ‘yan social media kulawa irin wannan me zai hana ba za’a yiwa ‘yan arewa??

Misali akwai tsarin Buhari New Media Center (BNMC) wanda ofishin hadimin shugaban kasa Bashir Ahmed ya samar, amma a binciken da nayi har zuwa yanzu da nake rubutu ba’a kaddamar da tsarin ba, shin don yana da nasaba da arewa ne akayi watsi da tsarin ko kuwa menene dalilin? domin muna gani akwai wasu ‘yan kudanci da suke gabatar da tsarinsu har fadar shugaban kasa aka kaisu akayi launching, laifin me ‘yan arewa sukayi da har za’ayi watsi da su a ki tallafa musu? a duk duniya babu wanda baya bukatar taimako, hatta ita kanta gwamnatin tana bukatar taimako

Don haka Maigirma shugaban kasa ina ankarar da kai domin ka fahimci wannan, domin gani nayi za’a samu matsala babba, mutanenmu na arewa musamman ‘yan uwa talakawa suna da bukatar a cigaba da wayar musu da kai imba haka ba ‘yan jari hujja su yaudaresu, idan kuma ba’ayi abinda ya dace ba to kada a ga laifin wadanda zasu ja baya daga tafiyar Buhari a socila media su koma ga ‘yan jari hujja wadanda suke nemansu dare da rana

Ina rokon Allah Ya sa wannan sakon ya kai har idon shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari

Leave A Reply

Your email address will not be published.