Video:- Dan Jarida Ja-afar Ja-afar A Kotu Ana Shari’a

Bayan Duk Gama Wasu Bincike Da Aka Dade Anayi Game Dan Mawallafi Yanar Gixo Ja-afar Ja-afar, Inda Hayaniya Ta Game Tsakanin Sa Da Gwamnan Jahar Kano Dr UMAR abdullahi Ganduje.

Ga Bayani Kamar Haka Tare Da Video NASA:-

– Mawallafin jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya bayyana gaban majalisar dokoki ta jihar Kano, da ke bincike kan zargin da ake yiwa gwannan jihar Kano

– A hannu daya kuwa, gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewar bidiyon ba na gaskiya bane, an yi amfani da kwamfuta wajen hada shi

– A ranar Alhamis dinnan ne, Mr Jaafar ya tsaya gaban majalisar, tare da yin rantsuwa akan cewa bidiyon na gaskiya ne ba hada shi akayi ba

Mawallafin jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya bayyana gaban majalisar dokoki ta jihar Kano, da ke bincike kan zargin da ake yiwa gwannan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na karbar cin hancin $5m daga hannun ‘yan kwangila.

Jaridar Premimum Times ta wallafa labarai daga bidiyon, wanda ta same shi daga Daily Nigerian, da ke nuna lokaci, waje da kuma yadda gwamnan jihar Kanon ke karbar daloli a matsayin cin hanci a wurare daban daban. Kudaden da Ganduje ya karba dai sun kai dalar Amurka miliyan biyar, daga hannun ‘yan kwangilar jihar.

Haka zalika gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewar bidiyon ba na gaskiya bane, an yi amfani da kwamfuta wajen hada shi, sai dai wani kwararre ya tabbatar da sahihancin bidiyon.

Babu karya a cikin bidiyon Ganduje yana karbar cin hancin $5m – Amsar Jaafar ga majalisar Kano

A ranar Alhamis dinnan ne, Mr Jaafar ya tsaya gaban majalisar, tare da yin rantsuwa akan cewa bidiyon na gaskiya ne ba hada shi akayi ba.

A yayin da ake jefa masa tambayoyi, Jaafar yaki bayyana wanda ya samar masa da bidiyon, wanda ke nuna Ganduje a lokacin da yake karbar cin hanci daga ‘yan kwangilar jihar.

Dauko :- Pressloaded Android App A Nan .apk

Download Video Now

Source www.Presshausa.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.