Karanta Yadda Wani Da Ya Cha-Chaki Mohammad Sala Da Yan Barcelona

Idan kana neman ‘yanci da Addinin kwallon kafa idan ka samu ‘yan Barcelona sai ka shafa fatiha,

ta karfi da Yaji nema suke su musuluntar da kwallon kafa, idan har suka ji baka goyon bayan M Salah a Final din da za’a taka yau a wajensu kai Munafiki ne makiyin Musulunci.

kuma suma ba don Allah suke goyon bayan M Salah ba, bakar hassadar su ce ga Real Madrid, kome zaku kira mu ku kira mu yau bama M Salah Ronaldo muke.
In har musulunci ne, babu wani club a Duniya da zai dagawa Real Madrid Hannu, munyi ‘yan wasa musulmai Daban daban, a yanzu muna da musulmai Irinsu Karim Benzema da Achraf Hakimi, dungurungum me Horar da Real Madrid din ma Musulmi ne Zidane (Zainuddeen Zaidan) har ayi mana Gorin musulunci.?
Hakika ina matukar son M Salah inason cigabansa da daukakarsa, naji matukar dadi da Nasarorin daya dinga Samu a baya, amma yau banawa Club dinsa fatan nasara, samun nasararsu Asarar mune, bakin cikin mune, rashin baccin mune, amma ina masa fatan bajintar da duniya zata yabe shi akanta, Allah yasa suna da rabo a shekara me Zuwa (shima idan an cire mu)

Idan ka tuhume ni akan kin nasarar musulmai mane da M Salah, kai ma zan tuhume ka akan kin nasarar benzema da Zidane domin suma musulmai ne. don haka Yau da yardar Allah sai Musulmi Zidane ya sake kafa sabon Tarihi na samun nasarar daukan Champions league sau uku a Jere, a wajen ku wannan ba nasarar musulunci bace???

Leave A Reply

Your email address will not be published.