An Yankewa Mutumin Da YaYi Wa ‘Yar Shekaru 9 Fyade

A yau Litinin, wata kotu da ke zama a yankin Kasuwan Nama a garin Jos da ke jahar Plateau ta yankewa wani direba mai shekaru 35, Ahmd Talib hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari bayan da ta kama shi da laifin yi wa wata yarinya mai shekaru 9 fyade,

Alkalin kotun, Yahaya Mohammed wanda shi ya yanke hukuncin bai baiwa Talib zabin biyan diyya ba, haka kuma ya bukaci ya biya N1300 kudin asibitin da aka kashewa yarinyar.

Alkali Mohammed ya ce wannan hukunci na shekaru hudu kacal zai zama izina ga sauran masu niyyar aikata irin wannan laifi.

Dan sanda mai kara, O.C Oche ya fadawa kotun cewa an kai masu rahotan faruwar lamarin ne a ranar 20 ga watan Maris a ofishin ‘yan sanda na Bukuru.

Ya ce wanda ake zargi wanda mazauni ne a yankin Akwan Doki a Bukuru ya ja hankalin yarinyar ne da biskit da kuma naira 200 zuwa shagon shi, inda ya yi mata fyade.

Talib ya amsa laifin shi tare da rokon kotun ta yi masa afuwa.

Laifin dai ya saba da sashe na 283 na kundin dokar ‘Penal Code’ ta Arewacin Nijeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.