Karya Ake Min, Ban Je Ganin Jonah Jang A Kurkuku Ba, Inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya, Atiku Abubakar ya musanta rahotannin nan da ke nuna cewa ya ziyarci tsohon gwamnan jahar Plateau, Jonah Jang a kurkuku.

Rahotannin da wasu gidajen jarida suka fitar su nuna cewa Atiku tare da wasu manyan kasar nan sun ziyarci Jang, wanda ke zaman kurkuku a yanzu haka.

Toshon gwamnan wanda hukumar EFCC ta gurfanar a bisa zargin badakalar kudade dai na zaman kurkukun ne a bisa umarnin kotu, kafin a kammala bukatar neman belin shi.

A wata sanarwa da ofishin Atiku ya fitar a safiyar yau Litinin, an bayyana rahotannin a matsayin na bogi.

Sanarwar ta bayyana cewa Atiku na Yola a jahar Adamawa tun ranar Alhamis inda ya ziyarta domin ya halarci bikin rantsar da shugaban jami’ar AUN.

Leave A Reply

Your email address will not be published.