Wata Mata Ta Yankwa Mijinta Al’Aura

Rahotanni daga jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, na cewa wata mata ta kashe mijinta bayan ta yanke ma sa mazakuta. ‘Yan sanda a jihar sun ce, matar ta kuma yi yunkurin kashe kanta amma makwabtanta suka shiga suka hana ta.

An dai yi amannar cewa, ma’auratan lauyoyi.

Kawo yanzu matar ada ake zargi ba ta ce komai ba kan wannan batu.

‘Yan sandan jihar sun ce, an kira su ne daga wani rukunin gidaje mai suna Diamond Estate da ke Ajah a yankin Lago a jihar ta Lagos da safiyar ranar Alhamis inda aka ba su labarin cewa wata mata ta kashe mijinta a rukunin gidajen.

Nan da nan ba a yi wata-wata ba, sai aka tura wasu ‘yan sanda wajen, inda da zuwansu suka tarar da mutumin a kwance cikin jini a kan gado.

Masu bincike sun ce, wadda ake zargi da aikata kisan ita ce matarsa, kuma ta yi amfani da wuka ne ta cakawa mazakutarsa a wurare daban-daban.

Kazalika ita ma ta yi yunkurin kashe kanta, kafin mutane suka hana ta.

Yanzu haka matar na asibiti tana karbar magani.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar ta Legas, Chike Oti, ya ce ma’auratan sun yi aure ne shekaru da suka wuce, to amma auren na cike da tashin hankali.

Ya ce tun lokacin da aka yi auren ba a zaman lafiya.

Irin wannan ya taba faruwa a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, inda ake zargin wata mata da kashe mijinta ta hanyar da ba masa wuka.

Lamarin dai ya faru ne a watan Nuwambar 2017, inda aka gabatar da ita a gaban kotu, kuma har yanzu ana shari’ar, ba akai ga yanke ma ta hukunci ba.

Sai dai matar mai suna Maryam Sanda, ta musanta zargin da ake yi mata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.