Sheikh Dahiru Usaman Bauchi Yace Dukkan Mabiyan Sa Su Fito Su Yanki Karin Zabe  { Don Kwatar ‘Yan Cin Mu }

Babban Malamin darikar Tijjaniyyar a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi karin haske kan kiran da yake yi wa mabiyansa na su fito kansu da kwarkwatansu wajen yankan katin zabe na dindindin domin takadarwa don yin amfani da wannan katin a zaben da ke tafe don aza nagartaccen mutumin da suka ga ya dace kuma zai yi musu aiyukan da suka kamata.

Shehu Dahiru Bauchi, wanda ya yi wannan karin hasken a hirarsa da manema labaru a gidansa da ke Bauchi a ranar Talatar nan, yana mai cewa, Nijeriya kasa ce wacce kowa na da ikon yin zaben da ya dace da shi domin kafa wanda zai biya masa dukkanin bukatunsa ta hanyar shugabanci.

Ya bayyana cewar ta wannan hanyar ne kadai dan Nijeriya zai iya yakar wanda bai so kuma cikin sauki domin a cewarsa zabar shugaba na gari tamkar bayar da dama ce wajen wanzar da shugabanci na gari, don haka ne ya umurci mabiyansa da cewa; “Dukkanin mutanenmu su fito su yanki katin zabe,” a ta bakinsa.

Shehi ya bayyana cewar kasar Nijeriya kasar su ce don haka suna da hakkin fitowa domin neman wanda suke so, hade da dabar mutumin da suka tabbatar zai yi musu aiyukan da suka zabe sa don su.

Ta bakinsa yake cewa Nijeriya musulmi da kirista kowa na da zarafin zabin da yake so ta fuskacin shugabanci, “Ai kasar Nijeriya ta musulmi ne da wanda ba musulmi ba; waye zai yadar da hakkinsa? Wani dai ba zai yada hakkinsa ba. tun da abun ya zama yakin da ‘yar karamar takarda ake yi bada makami ba; ai ya yi sauki, ka je ka jefa kuri’ar ka zabi wanda zai mallakeka wanda kuma kake ganin alamar zai biya maka bukatarka a zamanka na dan kasa,” In ji Dahiru Bauchi.

Bauchi ya daura kuma da cewa kuri’ar mutum makaminsa ce, domin da kuri’a mutum ka iya kashe kansa ko ya yanka kansa, don haka ne ya bukaci kowa ya yi amfani da wannan makamin tasa wajen zabar na gari, “Wai wasu ‘yan siyasa suna cewa kuri’arka-‘yancinka. Ni kuma ba haka nake cewa ba. ni ba dan siyasa bane, amma abun da na ke cewa, shi ne kuri’arka makaminka, wukarka ka bai wa wanda zai yanka ka ko kuma wanda zai yanka maka.

“Masoyinka wanda yake sonka zai yanka maka in ka bashi kuri’arka zai yanka maka, makiyinka ko kuma masoyinka na suna idan ka ba shi wannan kuri’ar to soyaka zai yi kuma ya yanka ka. Soboda haka ka san fuskokin mutune tun daga farko, ka san masoyinka ka san makiyinka. Dukkaninmu ‘yan Nijeriya mun san masoyanmu da kuma makiyanmu, mun san su, sai in lokacin kada kuri’ar idan ya kammala yi sai mu kada ma wanda muke so,” in ji Shi.

Daga bisani ya kuma nemi dukkanin wani dan Nijeriya da ya fito fagen zabe domin zabar na gari a kowani lokaci.

Da ya juya kan shuwagabanin kuwa, Shehu Dahiru Bauchi ya gargadi shugabanni kan wadanda suke shugabanta domin a cewarsa kowani shugaba ya dace ne ya tabbatar da cika alkawuran da ya yi wa jama’arsa a lokacin yakin neman zabe “Ainuhin abun da ake nufi da gwamnati musamman gwamnatin siyasa, jama’a ne idan suna da wasu abubuwan da ba za su iya samu ba sai su nemi gwamnati ta hanyar siyasa, su kuma ‘yan siyasa za su nemi yin aiyukan da za su kare mutane daga sharri da kuma samar musu da alherin da suke bukata. in an zabi gwamnati ba ta kawo alheri ba sai sharri, ba ta ture sharri ba sai alheri ta ture wannan ai ba gwamnati bace, a don haka ne muke jawo hankulan mutane su yi karatun ta nutsu,”.

Ya bayyana cewar duk wanda ya fito gaban jama’a aka kada masa kuri’a ya ci ya kamata ya yi dukkanin mai iyuwa domin rage wa jama’ansa matsatsin da suke ciki “Ana wahala don haka muna kira ga gwamnati ta yi duk mai iyuwa domin rage wa jama’a halalhalun da suke ciki domin a samu gudunar da shuganci yadda ya dace,” kamar yadda ya ce.

Leave A Reply

Your email address will not be published.