Za’aga Taro Ranar JAMA’A Mai Zuwa Nawa Kasa Addu’a inji Sheikh Dahiru Usaman Bauchi

Babban Shehin Darikar Tijjaniyya a Afirka, Shehu Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewar a kowace ranar 15 ga watan Rajab na kowace shekara su kan hadu domin gudanar da gagarumin maulidin Shehu Ibrahim Inyas wanda ke hada fuskokin miliyoyin jama’a daga sassa daban-daban na duniya.

A taron na bana wanda aka tsara cewar zai gudana ne a birnin tarayyar Nijeriya Abuja a ranar Asabar din nan da ke tafe, zai kuma samu cinkoson jama’a domin halartar gagarumin taron maulidin wanda aka saba shekara-shekara.

Shaikh Dahiru Bauchi, wanda ke bayyana yanda taron zai gudana a hirarsa da manema labaru a daren ranar Lahadin nan da ta gabata, a gidansa da ke Kofar Gombe a cikin garin Bauchi.

Ya yi bayanin cewar a bana za su gudanar da taron ne a Abuja a maimakon wasu garin, ya kuma ce daukan wannan matsayar na zuwa ne domin a nuna wa duniya girma da daukakan Shehu Ibrahim Inyas.

Tun da fari ma, Dahiru Bauchi ya bayyana cewar ita maulidi ana yin tane domin nuna godiya wa Allah da samuwar bayin Allah na gargaru da kuma salihan bayi, ya bayyana cewar suna taron tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah, don haka ne kuma suke taron tunawa da ranar da aka haifi magadansa, ya ce soyayya da godiya wa Allah ce manufarsu a kowace lokaci na yin irin wannan taron.

Ta bakin Shehu Dahiru, koda yake ya ce da ba a Abuja za su yi ba; amma sakamakon wasu abubuwa ne ya sanya suka sauya taron zuwa Abuja “Maulidin na bana ya samu wani irin salo ne, wasu jama’a sun bayar da shawarar cewa a yi taron a Taraba ni kuma na ce a’a ba za a yi a Taraba ba, sakamakon bala’in da ya samesu na kashe-kashen jama’a da dabbobi ba za mu kara daura musu wasu dawainiyar baki ba kuma, da muka ce haka, sai mutanen Kaduna suka nemi a yi musu taron a garinsu, wasu kuma su ka nemi a yi taron a tarayyar Nijeriya Abuja suka kawo hujjojinsu masu karfi sai muka amsa wannan,”

Ya bayyana cewar har zuwa lokacin da ke ganawa da manema labaru a daren ranar Lahadi dai a matsayar da ake yi kenan, ya kuma bayyana cewar shi Kalifar Shehun bai nuna cewar sai a Kaduna ko Abuja za a yi taron maulidin ba; amma Shehu Dahirun ya karfifi batun cewar a Abuja ne taron zai wakana.

Bauchi ya ce kila Shehun ne ke neman bayyana girmansa a wannan duniyar “Kamar dai Shehu din ne yake son ya nuna bunkasarsa na cewa bana yana son a yi maulidin nasa fiye da kullum; to duk da na kullum (kowace shekara ke nan) ana haduwa a yi a waje daya, amma bana wasu Samari sun shigo da wasu abubuwan da ba a jin dadinsa cikin lamarin, shi kuma wannan lamarin ba na samari ba ne, bana yara ba ne . lamari ne na Kalifofin Shehu da Kalifan Shehu, don haka babu yadda za a yi wani daga cikin Almajiran Shehu ya yi jayayya da Kalifan Shehu na Kaulaha ba zai iyu masa ba, ba kuma dai zai iyu ba ne. A don haka mu girmama wa ne a garemu, dan Shehu wanda ya zama abun girmamawa a garemu ba abun jayyaya ba ne,” In ji Dahiru Bauchi.

Ya daura da cewa, “Yanzu dai matsayar da ake ciki kenan, wasu na cewa a Kaduna wasu na cewa a Abuja, amma kafin lokaci ya zo za mu san yadda za mu yi, tun da abun namu ba na gaba ba ne, bana fada ba ne, ba kuma na raina juna ba ne, abu ne na nuna soyayya ga Shehu Ibrahim (R), shi abu in za a yi don Allah an wuce wahala domin shi Allah yana ganin zuciyar kowa, duk wanda yake son shigo da wani rudani sai ka ga Allah ya dawo mana da shi alkairi,” In ji Malam Dahiru Bauchi.

Shaikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewar yanda shakalin bikin zai wakana a birnin tarayya Abuja dai bai wuce yadda aka saba yi a shekarun baya ba, yana mai cewa za su nemi izinin jami’an tsaro, gwamnati da kuma neman muhallin da za a yi wannan taron, kana da kuma neman jami’an tsaron da za su dafa domin bayar da tsaro mai nagarta.

Ya yi amfani da wajen taron manema labarum wajen kira ga jama’a da su amshi bakinsu hanu biyu-biyu domin faranta wa bakin da za su zo Abuja rai wa wannan gagarumin taron maulidin Shehu Ibrahim Inyas.

Dangane da hasashen miliyoyin jama’an da za su halarci wannan taron, wadanda za su yi wa Abuja kawanya domin wannan maulidin kuwa, Dahiru Bauchi ya bayyana cewar tsabaragen yawansu ba mai misaltuwa ba ne “Aaaa! Ai ba mu da alkalumar da za mu bayar na cewar mutanen da za su halarci wannan taron za su kai kaza, domin duk lokacin da aka yi taron maulidin sai a ga taron ya fi karfin taron da aka zata za a yi a kowace gari ne kuwa aka yi taron maulidin Shehu, duk inda aka je sai a samu taron yafi karfin yadda ake tsammata,”

Ya kuma yi bayanin cewar miliyoyin jama’a daga cikin garuruwan Nijeriya, kasar Nijeriya da wasu kasashen waje ne za su zo domin halartar wannan taron, ya bayyana cewar suna da manyan baki daga kasashe irinsu Kaulaha (Senigal) da irin su kasar Maroko, Aljeriya, Masar, Sudan, Chadi, Ghana, Kamarun da sauran kasasshen da za su zo domin halartar wannan taron da za a yi a birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewar taron za su gudanar da shine ranar Asabar, amma kuma za a fara shagalinsa tun daga ranar juma’a domin za a yi zikirori domin yi wa kasa addu’a.

Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira da a zauna lafiya a tsakini, Dahiru Bauchi ya bukaci jama’an kasar nan da su sanya tsoron Allah a matsayin hanyarsu a kowace lamari domin dacewa da abubuwa masu kyau a rayuwarsu.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana wa jama’an cewa za su ga yawan motoci masu zirga-girga a ‘yan kwanakin nan don haka yana mai shaida wa jama’an kasar nan cewar gagarumin taron da suka saba yi ne duk shekara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.