Yaki Da Cin Hanci Tilas Ne Ba Zabi Ba –Magu

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Malam Ibrahim Magu, ya bayyana cewar, yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya yaki ne na tilas ne ba na ganin dama ba, don haka babu wani abn da zai tsaida hukumarsa daga cigaba da yaki da rashawa da cin hanci a fadin kasar a kowane yanayi ne kuwa.

Mr Magu, wanda ke tattaunawa da manema labaru a jiya Asabar a birnin tarayya Abuja, bayan bude taron da Bureau of Public Procurement (BPP) wacce ta shirya wa shuwagabanin bangarorin ma’aikatun gwamnati, ya bayyana cewar, yaki da rashawa ba aikin zabi ba ne, ya bayyana cewar dole ne kawai ya yaki rashawa.

Ta bakinsa, “Mu muna kan yakar rashawa ba tare da jinkiri ba; yaki da rashawa babu wani abun da zai tsaida mu daga kokarinmu ya kawar da rashawa da cin hanci. Ina sake nanatawa, babu wani abun da ya isa ya tsayar da mu daga yaki da rashawa a kowani yanayi ne kuwa,” ya shaidar.
Shugaban hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa, Magu ya ci gaba da cewa a yanzu haka hukumarsu tana ci gaba da kokarinta na tabbatar da share dukkanin wani nau’i na cin hanci da rashawa, ya bayar da tabbacin cewar nan gaba kadan cin hanci da rashawa zai zama tarihi a Nijeriya.

Kamar yadda Magun ke cewa, EFCC ba tana yaki da cin hanci da rashawa ne kawai a matsayin abun da ta zabi ta yi ba, ya bayyana cewar doka da oda ne suke bi wajen kawar da barayin dukiyar kasa da masu zagon kasa wa tattalin arzikin kasar.

Ibrahim Magu, ya kirayi dukkanin wani mai kishin kasa da kuma son ci gaban Nijeriya day a bayar da tasa gudunmawar wajen yaki da cin hanci da rashawa domin kubutar da Nijeriya daga halin da take ciki na masu wawuso da dukiyar kasa, hade da kokarin kwato dukiyar da wasu daidaiku suka kwakwashi na jama’a.

Ya ce, ba kawai jama’a za su zuwa wa EFCC ido bane, suma suna da gudunmawar takawa wajen yaki da rashawa da cin hanci a kasar nan.

Da yake jawabi a wajen bude taron, Babban sakataren gwamnatin tarayya, (SGF) Mr Boss Gida Mustaph, wanda ya samu wakilcin sakataren ofishin SGF, Mr Olusegun Adekunle, ya gargadi ma’aikatun da ba na gwamnati ba da kuma masu kwangila da ‘yan kasuwa da basu yi rijista na hakikani bad a cewar su mutunta matakai su yi rijistansu yadda ya dace.

Ya bukaci masu samun horon da su maida hankula domin koyon abun da ya dace da kuma yin aiyukansu da sukace.

Leave A Reply

Your email address will not be published.