Ma’aikatan N-Power Sun Amshi Wayoyi A Ofishin MTN

Matasan da su ka amfana da tsarin N-Power sun cika da farin ciki da annashuwa gami da godewa gwamnatin shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, yayin karbar wayar hannu da a ka yi musu alkawarin za a ba su kuma a ka cika a gidajen sadawar na MTN, wadanda su ke raba wayoyin. Don haka kowanne gidan waya na MTN a cike ya ke makil da ma’aikatan N-Power, domin karbar wayoyin nasu.

A yadda tsarin ya ke, da ma ba za ka je wajen ba ma sai ka sami rubutaccen sako daga hukumar N-Power, sannan a rubuta ma ka ofishin MTN mafi kusa da kai da kuma kwanan watan da za ka je.

Wayoyin da ake rabawa sun bambanta da juna. Akwai Samsung tab E, plus E signature, Afrione, speech tab da RLG mate.

Tun watannin baya da su ka wuce ne ma’aikatan N-Power da dama su ka karbi tasu har ma tuni sun fara amfani da ita. Wadannan su ne rukuni na farko, yanzu kuma rukuni na biyu ne su ke karba daga 4 ga Afrilu, 2018, zuwa lokacin da su ka kammala karba.

Babbar shaidar da za su nuna ita ce, rubutaccen sakon da aka tura mu su daga N-Power, sai kuma katin ‘BBN da shaidarka.

Ba a sami matsaloli wajen karbar wayoyin ba, amma mutane kalilan sun sami matsala, wasu sun je ba tare da an tura musu rubutaccen sakon ba, sannan kuma wasu ba su dora hotonsu da katin shaida akan fejinsu ba yayin cike fom din zabar wayar. Don haka an dawo musu da takardunsu har sai sun gyara.

A garin Kano ranar 5 ga Afrilu, 2018, tun da sanyin safiya da misalin karfe bakwai ma’aikatan N-Power su ka cika ofishin MTN mai lamba 2A da ke kan titin Cibic Center bayan Post Office a, don karbar wayoyinsu.

Ma’aikatan MTN su na yin matukar kokari wajen ba da lamba, don shiga ciki a nutse, ba a rufe bayarwa ba har sai bayan karfe hudu zuwa biyar na yamma.

LEADERSHIP A YAU LAHADI ta ziyarci wajen inda ta samu zantawa da wasu daga cikin wadanda su ka amfana. Ga yadda tattaunawar ta kasance tare da wasu mata da maza daga cikin wadanda su ka ci moriyar abin:

Mu Na So A Dauke Mu Aiki Dindindin –Fari’atu Bashir

Za mu so mu ji sunanki da matakin karatunki?

Sunana Fari’atu Bashir Abubakar. Ina da digiri.

A N-Power wanne bangare ki ke?

Ina N-Tech. Ina koyarwa a gidan makama a karamar hukumar birni, KMC.

Ga ki a layin karbar waya za ki shiga ki karba. Me za ki iya cewa?

Mu na farin ciki tunda an yi ma na alkawari kuma an cika. Akwai rukuni na farko da su ka fara karba. Batch A kenan. Mu ne Batch B. Na sami sako a wayata tun sati biyu da ya wuce a kan yau na zo na karba. Yanzu ga shi mun zo an ba mu form mun cika sun shiga ciki da shi ba su fito ba, amma za su fito su kira sunaye.

Wanne sako ki ke son mikawa ga shugabanni N-Power?

Mu na godiya kwarai da gaske ga shugaban kasa. Duk alkawuran da ya yi ma na ya na cikawa, kudinmu a kowanne wata ya na shigowa. Mu na son mu sami wani aiki kwakkwara. Ba ma so mu dogara da wannan aikin na N-Power mai takaitaccen lokaci.

Kenan ki na fatan idan kun gama a dauke ku aiki na dindindin?

Eh! Mu na so a dauke mu a matsayin ma’aikata na dindindin, amma a bambance masu digiri, masu NCE da ’yan sakandire wajen biyan albashi, idan za a kara albashi.

Mun gode.

Ni ma na gode.

Baba Buhari Ya Cika Ma Na Alkawari –Aishatu Aliyu

Za mu so mu ji sunanki da matakin karatunki?

Sunana Aishatu Aliyu Usman. Ina cikin tsarin N-Tech. Ina da NCE, Ina koyarwa a karamar sakandare ta Kansakali.

Ga ki a layi, za ki karbi waya. Me za ki ce?

Mun godewa Allah, mun godewa gwamnatin Baba Buhari duk alkawarin da ya yi ma na ya cika. Ga albashinmu ya na shigowa kowanne wata. Mu ne Batch B. Ga shi yanzu mu ma an kira mu an karbi takardunmu, an shiga ciki mu na jira. Don duk na gabanmu su na ta karba su na fitowa dauke da wayoyinsu.

Akwai sakon da ki ke so ki aika?

Shugaban kasa Baba Buhari tabbas ya taimakawa al’umma da wannan abu da ya samar ma na. Ina fatan Allah Ya sa a dauke mu aiki na dindindin.

Ki na so a bar ki a inda ki ke ko ki na fata a canja miki ma’aikata?

Kowanne a ka ba mu za mu yi farin ciki.

Albashin da a ke ba ku, ya na taimaka mu ku kuwa?

Ni dai a wajena ya na taimakawa sosai ma kuwa, saboda a da a haka mu ke zaune babu aiki babu mai taimaka mana.

Mun gode.

Ni ma na gode.

Mu Na Fata Shirin N-Power Zai Dore –Ibrahim Sha’aibu

Yaya sunanka da matakin karatunka?

Sunana Ibrahim Sha’aibu. Ina da NCE, ina bangaren N-Tech. Ina koyarwa a firamare ta Model Dawakin Tofa.

Ga ka da waya a hannunka. Me za ka iya cewa?

Ina godiya ga Allah (SWT) da Ya kawo mu wannan rana da na karbi ‘tablet’ dita. Ita ce na’urar da za ta taimaka wajen gudanar da aiki na N-Power. Shi dai wannan tsari ne wanda gwamnatin tarayya ta kirkiro da shi domin taimakawa matasa.

Wacce iri aka ba ka, don na ga wayoyin kala-kala ne?

Eh, an ba ni Samsung Tab E, kamar yadda ki ke gani ga ta a hannuna. MTN kuma sun hada mana da layin waya. Yanzu mu na jira a yi mana rajista dinsa ne.

Wanne sako za ka aika ga shugabannin N-Power?

Sakona ga shugaban kasa shi ne mu na fatan yadda aka fara, a karshensa za a mayar da ma’aikata da ke ciki ma’aikata na dindindin, domin gaskiya za a iya samun matsala idan a na turo ma sa albashi daga baya a ce an daina. Kirana ga gwamnati ya zamana ta bawa matasa aikin yi.

Kudin da a ke biya ka na ganin ya na taimaka mu ku?

Ya na taimakawa sosai kasancewar wasu daga cikinmu ma ba su taba samun wani aiki da aka taba biyansu Naira 5,000 a dunkule ba, amma yanzu ya zamana a na biyan su Naira har 30,000 a wata. Kudaden nan ya na taimawa wajen yin wasu abubuwan na rayuwa, sannan an rage zaman banza da matasa su ke yi.

Na gode.

Ni ma na gode.

Ina Fata Buhari Zai Mayar Da Mu Cikakkun Ma’aikatan Gwamnati –Adamu Fagge

Yaya sunanka da matakin karatunka?

Sunana Adamu Bala Fagge. Ina da digiri, Ina karkashin N-Tech. Ina koyarwa a Junior Secondary School da ke bangaren Fagge. Ina koyar da ‘Basic Science’ a wannan makaranta

Ga waya a hannunka. Me za ka iya cewa game da wannan?

Ga Samsung Tab E a hannuna; gaskiya ina cikin farin ciki. Babu abin da za mu ce sai dai mu ce Allah Ya saka da alkhairi. Mu na mika godiyar mu zuwa ga shugaban kasa; Allah Ya saka masa da alkhairi, don ya dauki dawainiya, ga shi an ba mu tab za mu cigaba da aiki. Mu na yi ma sa fatan alkhairi da fatan Allah Ya kara lafiya, Allah Ya biya ma sa bukatunsa na alkhairi, Allah Ya dafa masa a cikin shugabancinsa.

Kenan duk alkawuran da a ka yi mu ku a na cikawa?

Gaskiya a na cikawa, a na biyan mu albashi duk wata ga kuma waya an ba mu.

Me nene fatanka a nan gaba?

Fatana ba ya wuce yadda mu ka fara abin nan mu na fatan shugaba kasa, mun san shi da kishin matasa, mu din nan gabadaya matasa ne, wannan aikin da mu ke yi ya na taimaka ma na wajen kula da iyali. Kamar ni din nan Ina da aure, Ina da yaro daya, Ina ciyar da iyalina, Ina taimakon iyaye da ’yan uwana da wasu mutane ma daban duk da kudin N-Power; mu na fatan a rike mu a matsayin ma’aikata na dindindin. Ina da yakinin shugaban kasa mai adalci zai yi ma na wannan alfarma.

Mun gode.

Ni ma na gode.

Leave A Reply

Your email address will not be published.