Karanta Nazarin Asalin Hausa A Duniya

Farfesa Umar El zakzaky Al Bahaushe yace” kwayoyin halittar Fir’auna Seti, wannan daya yayyanka yahudawan zamaninsa, da kuma na magajinsa Fira’una Remesis II, wanda yayi zamani da Annabi Musa A.S sunyi kamanceceniya da kwayoyin halittar mutanen kano na yau, musamman ma nacikin kwaryar badala.”

Sai dai Farfesa Muzzah Jibrin, Farfesa Abdullahi Elkanawy da wasu masana da dama sunyi watsi da wannan bincike. Ga abinda ya fito daga makalar masanan kamar yadda suka gabatar a wani taro daya gudana a Arewa House dake kaduna:

Kuskure ne a hada asalin wancan Fir’aunan da kano tunda Gawar Mornoptah, dan Fir’auna Remeses II, fir’aunan da aka halakar a ambaliyar ruwa yayin da yake bin sawun Annabi Musa A.S don ya halaka shi, wadda Masani Loret ya gano a shekarar 1898 a tsohon birnin Thebes ta nuna cewar kwayoyin halittar ta sunfi kamanceceniya dana mutanen egypt ne ba mutanen kano ba”.

A wani kaulin kuma, masanan sunyi hasashen cewa kwayoyin halittar mutanen zariya dana kabilar Gwari da Igala suma sunyi kamanceceniya da juna, wanda hakan na nuni da cewar kodai kabilun asalinsu a zariya suke da zama, ko kuma al’ummar kabilun ne suka kafa garin na zaria lokaci mai tsawo daya shige, don haka yanuwan juna ne kenan. Muna kuma iya cewa daga jikin mutum guda kabilun suka fita.

Amma maganar su da sukace sun auna wasu buraguzai na kasusuwan mutanen dake kwance a wasu makabartu a kano, har kuma sun gano cewar mafi yawan kwayoyin halittar mutanen kano yafi nuni dana Sharifai, kamar akwai siyasa a ciki.

Tabbas, tarihi ya nuna cewar a wajajen karni na goma sha uku, wangarawa karkashin Sheik Abdurrahman Zaiti tare da wasu malamai kimanin arbain irinsu Modibbo sheshe, Mandawari, Limamin Madatai, Limamin Jujin ‘yan labo sunzo kano har ma suka kawo musulunci garin. Lokacin Sarkin Kano Yaji dan Tsamiya ke bisa gadon sarauta.

Sai kuma a karni na goma sha biyar zamanin Sarkin Kano Rumfa Akace wani balarabe masani mai suna Imam Maghili ya ziyarci kano shima da wasu jama’a tasa. Daga baya ma ance yabar wasu daga zuriyarsa anan kano, wadanda su ake kira Sharifai zuwa yanzu.

Marubuci, marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya kawo wata muhimmiyar gaba a shafi na 22 na littafinsa mai suna Wangarawa Sun iso Kano, inda yake cewa “Sheik Abdullahi Ilorin ya nuna cewar tun a karni na goma sha daya wangarawa suka fara bazuwa suna yada musulumci a afirka ta yamma. Yace su wangarawa kasarsu ta farko misira(Egypt). Yace asalin mazaunan kabilar Sundiata da asalin kabilar Kakan Mansa Musa da asalin kabilar Songhai irinsu Askiya Muhammad kenam, tarihi ya nuna duk a misira suke kafin su iso Mali, inda mafi yawan masu tarihi ke cewa daga Mali wangarawa sukazo, amma Mali din ma zuwa sukayi”.

Sai dai, koda auratayya ta wanzu tsakanin wangarawa da larabawan da suka sauka a kano da kanawa bakaken fata na lokacin, da wuya ace an samu kwayoyin halitta sunyi irin wannan mamakon rinjayar. Domin kuwa kano tun asali garin bakaken fata ne ba farare ba, ba kuma a taba samun cewar an maye mutanen kano da wasu mutanen ba, don haka fadin cewar kwayoyin halittar kanawa ya nuna su sharifai ne ba lalle ya zamo ya inganta ba.

Amma tana iya yiwuwa, anyi rashin sa’a, buraguzan da aka samu a makabartun wadanda akayi wannan gwajin dasu (sample) na Wangarawa da larabawan ne dana zuriyarsu wadanda watakila sun cakudu da bakaken fata, don haka binciken bai iya bada labarin daukacin mutanen kano ba, tunda dokar irin wannan binciken ta nuna cewa wajibi ne abubuwan da za’ayi bincike akansa su zamo suna wakiltar daukacin abinda ake magana akansa.

Wani abin lura ma anan shine shigar siyasar addini a cikin dukkan binciken.

Mun ji bincike na farko ya nuna cewar Fir’aunan daya kashe jarirai dan kano ne, don haka wasu ke ganin hakan kamar kaskanci ne ga kanawa, shiyasa sukuma suka wanke kanawa da cewar asalinsu sharifai (jikokin fiyayyen halitta) ne..

A hakika dai, bamu da karan nunawa ga wadancan Malumma masu girma, amma wajibin mune mu karbi gaskiya komai dacinta dangane da asalin mu. Maganar addini ba zata sa mu boye asalin muba, tunda da ayyukan mu akace za’ay mana hisabi bada asalin muba. Rashin ingancin binciken na farko shine kurum hujjar da zatasa muki aminta dashi amma ba laifib da firaunan ya aikata ba.

Akwai binciken masana dake cewa Kwayoyin halittun Firauna Remesis II yafi kamanceceniya da kwayoyin halittun mutanen Afirka ta tsakiya a ma’auni na farko, daga nan sai mutanen kasar south Africa a ma’auni na biyu, sannan mutanen Afirka ta yamma inda hausawa suke a ma’auni na uku. Wanda hakan ke nuna alakar hausawa da wancan firauna tayi tazara da shekaru masu nisan gaske… (Watakila sai kowacce kabila daga cikin biyun ta tike da Annabi Nuhu ko Annabi Adamu za’a diga aya)

Sai dai kuma, akwai tsohon zance dake nuna kwararowar misirawa izuwa yankin afirka ta yamma a tsahon zamani daya shude. Watakila tun zamanin Annabi Musa A.S hakan ta faru, ko kuma wani lokaci kafin haka, domin kuwa labarin baka yana nuna cewar garin Auyo dake jihar jigawa ya kafu tun kafin Haihuwar Annabi Musa A.S, sai dai kuma karancin tarihin da muke dashi akan kabilar Auyokawa da akace sune suka kafa garin ke hanamu gane alaka ta jini ko ta sadarwa da wayewa a tsakanin mutan garin da kuma misira tun a wancan tsohon zamani.

Leave A Reply

Your email address will not be published.