AN FITARDA SAKAMAKON ZAMANDA AKAYI AGIDAN KHALIFA SHAIKH ISHAQA RABIU KANO (RTA) AKAN MAS`ALAR MAULUDIN SHEHU (RTA)

Alhamdulillah, Bayan Gabatar Da Wannan Zama, Na Bazama Bincike, Domin Jin Takamaiman Abinda Aka Tattauna, Cikin Huwacewar ALLAH Kuma Nasamu Zantawa Da Mutum Biyu, Daga Cikin Wadanda Akayi Zaman Dasu, Kuma Ga Labarin Da Suka Labarta Mun Bisa Harshen Gaskiya Da Amana.

Anyi Zama Cikin Mutumtawa Da Girmamawa Tsakanin Maulan Mu Sheikh Ishaqa Rabi’u Da Kuma Assayyadi Alhaji Ibrahim Bn Maulana Sheikh Dahiru Bauchi (rta).

Maulaya Sheikh Ishaqa Rabi’u (rta) Yayi Matukar Farin Ciki, Da Yadda Alhaji Ibrahim Yadinga Mutumtashi, Da Kiran Sa Da Sunan ” Baba” Tare Da Girmama Shi Tamkar Yadda Yake Girmama Mahaifin Sa, Maulan Mu Sheikh Dahiru Bauchi (rta) Wannan Al’amari Yayi Matukar Farantawa Maulana Sheikh Ishaka Rabi’u Rai, Har Ma Da Bayyanar Matukar Farin Ciki A Fuskar Sa..

Dayawa Daga Zantukan Da Ake Yadawa A Gidajen Redio, Da Nan Social Media, Da Suke Nuni Da  Rikici, Tsakanin Janabin Maulana Sheikh Dahiru Bauchi (rta), Da Kuma Sheikh Ishaqa Rabi’u (rta) , Bada Yawun Dayan Su Ake Yi Ba, Hasali Ma Su Basu Sanda Anayin Hakan Ba, Illadai Masu Yin Sunayi Ne Domin Cimma Wata Manufar Su Ta Siyasa,  Hatta Cikin Takardun Da Aka Bubbuga Aka Sanya Sunan Maulana Sheikh Ishaqa Rabi’u  Akan Wannan Mas’ala Ta Mauludi, Tare Da Cewa Daga Shi Suka Fito,Dayawa Baima Sanda Su Ba. Hasali Ma Shi Baya Kasar Duk Hakan Take Faruwa.

Sannan Sanarwar Da Ake Fitarwa Cewa Maulana Sheikh Ishaqa Rabi’u Yace A Kaduna Za’ayi Mauludi, Kuma ‘ya’yan Shehu Ma Kaduna Zasu Zo, Wannan Duk Karfaganda Ce Wacce Sheikh Ishaqa Rabi’u Bai Sanda Ita Ba Kuma ‘Ya’yan Shehu Ma Basu Sanda Wannan Zance Ba.

DANGANE DA MATSAYA AKAN BATUN MAULUDIN SHEHU KUWA..

Bayan Sheikh Ishaqa Rabi’u (rta) Ya Saurari Alhaji Ibrahim Bin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (rta) Tare Da Jin Hikima, Da Maslahar Da Yasa Maulan Mu Sheikh Dahiru Bauchi (rta) Ya Mayar Da Mauludin Shehu Zuwa Abuja, Kuma Yayi Masa Kyakkyawar Fahimta, Sai Ya Tambaye Shi Matakin Da Ya Dace Adauka, Sai Alhaji Ibrahim Yace ” Baba Duk Abinda Ka Zartas Shine Daidai Agare Mu”.

Sai Sheikh Ishaqa Rabi’u Ya Tura Alhaji Ibrahim Zuwa Khaulaha, Wajen Sheikh Tijjani Inyass (rta) Domin Gaya Masa Abinda Suka Tattauna Dashi, (Wanda Yazamo Bayani Ne Na Sirri A Tsakanin Su) Sannan Kuma Sheikh Ishaka Rabi’u Ya Buga Waya Ga Sheikh Tijjani Inyass (rta) Tun Gabanin Saukar Alhaji Ibrahim, Domin Shaida Masa Shine Ya Aiko Alhaji Ibrahim Ibn Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (rta) Da Sakon Sa..

Abinda Aka Tabbatar Mun Shine, A Hukumance Za’a Bayyana Garin Da Za’ayi Mauludin Shehu, Ranar Laraba, Insha ALLAH Domin A Ranar Ake Kyautata Zaton Dawowar Alhaji Ibrahim Da Matsaya Guda Daya Da Sheik Tijjani Niasse (rta) Ya Tsaida Kuma Ya Zartas..

Wato Dai A Halin Yanzu Sai Ranar Laraba Za’aji Takamammiyar Matsaya Da Aka Cimma A Hukumance, Wanda Muke Kyautata Zaton Dukkanin Tijjanawa Zasu Kasance Masu Karbar Sa Hannu Bibbiyu Da Daukar Kaddara, Dayiwa Shugabanni Da’a Cikin Abinda Ake So Da Wanda Ba’a So.

DUK WATA SANARWA DA AKAJI WASU SUNA YAYATAWA, SUNA ZARTAS DA AL’AMARI NE YADDA YA DACE DA SON ZUCIYAR SU, AMMA ASANI BA DAGA WADANNAN JAGORORIN YA FITO BA.

MUNA ROKON ALLAH (SWT) YA HADA KAN TIJJANAWA, YA SHIRYI WADANDA BABU DARE BABU RANA SUKE BEGEN GANIN AN SAMU FARRAQA TSAKANIN MABIYA, ALHALI SU JAGORORI SUN KASANCE AMINAI NE MASU MUTUMTA SASHEN SU ZUWA SASHE.

ALLAH YASA MUDACE!aji Takamammiyar Matsaya Da Aka Cimma A Hukumance, Wanda Muke Kyautata Zaton Dukkanin Tijjanawa Zasu Kasance Masu Karbar Sa Hannu Bibbiyu Da Daukar Kaddara, Dayiwa Shugabanni Da

Leave A Reply

Your email address will not be published.