Buhari Yayima ‘Yan Matan Dapchi Tarbon Karamci A Fadar Sa ( Hotuna )

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan matan Dapchi da Boko Haram suka sako bayan da suka sace su daga makarantar da suke ta kwana, a jawabin da yayi a gurin ganawa da yayi da ‘yan matan shugaba Buhari ya bayyana farin cikinshi da sakinsu da Boko Haram suka yi ba tare da wani sharadi ba.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa gwamnati bata biya Boko Haram ko sisi ba akan sakin ‘yan matan, sunyi tattaunawa dai wadda gashi anga sakamakonta, shugaba Buhari ya kuma godewa ‘yan Najeriya da suka taya da addu’o’i da kuma jami’an tsaro wanda suke aiki ba dare ba rana.

Haka kuma yace an baiwa kowane shugaba rundunar tsaro gargadi me tsauri na cewa ya kula da yankin da aka bashi tsaro da kyau domin duk abinda ya faru ba za’a daukeshi da wasa ba.

Shugaba Buhari ya tabbatarwa da ‘yan matan na Dapchi cewa su kwantar da hankalinsu zasu yi karatu cikin yanayi me kyau domin yanzu an saka jami’an tsaron da zasu kila dasu. Haka yayi gargadi ga masu neman su mayar da abin siyasa da cewa su kuka da kansu dan ba za’a lamuntaba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.