Rarara Ne, Jigo Uban Tafiyar Neman Zaben Baba Buhari Tin Daga Bakin 2015 Zuwa 2018

Rarara yayi amfani Hazakarshi Da Kuma Basirar shi domin Karfafa ba Matasa Gwiwa da wakar shi da yayi mai taken (Mai Malfa Ya Karaya) a lokacin da aka daga zabe wakar tayi tasiri sosai ganin yadda Matasa suka Zabura Domin Su za an chanza…

Download MAI MALFA YA KARAYA Music
Sannan Bayan Haka Rarara bai tsaya ba ya kara yi ma Buhari Campaign da Wata wakar shi mai Taken (Fadan Karshe) inda Rarara Yayi amfani da Basirar shi wurin rera wannan Wakar Domin wakar tayi tasiri a zuciyar matasa, har ma da tsoffi Rarara ya fada ma mutane zaben fah shine fadan Karshe idan akayi Sake za’kasa…

Downlaod FADAN KARSHE Music  

Duk da haka Rarara bai daina taimaka wa Buhari ba har bayan zabe wurin yada Labarai tun kafin a Nada Lai Muhammad a matsayin Minister Information and culture Rarara ya fitar da Wata waka mai taken MASU GUDU SU GUDU ya shirya ma wannan wakar sosai Domin yayi tunani a wajen rera wakar Rarara ya Isar da sako Ga Mutanan Nigeria inda yake nuna ma Wanda sukayi satar kudin Nigeria fah Buhari ya karbi kasa don Haka Duk Wanda yayi sata ya Gudu.

Download MASU GUDU SU GUDU Music…. 

Wakar Masu Gudu Su Gudu gaba dayan ta nazartu Ne a wani baiti Wanda Rarara ya Isar da sakon shugaba buhari,  baitin nan har yau mutane na tunanin shi saboda abunda Rarara yace shike faruwa yanxu haka Ga baitin kamar haka:-

* Al’umma na kasa Ku taho kuji Labarin da ake

* General ya karfi kasa amma fa kusan halin da take

* Farko Ga cin Hanci ya yadu akan layin da muke 

* Curruption yayi yawa Su dan baki ban kaurar su suke

* An kasa a bamu tsaro kullum ibar rayin mu ake

* Tattali arziki na kasa duk ya rushe maganar da ake

* harkar noma zero, wuta, da ruwa hanya a hake

* Harkar ilimi zero kullum yajin aikinsu suke

* Kuma Fannin na lafiya likitoci zaluntar su ake

* Muna ta bikin murna amma fah kusan halin da muke 

* General ya karfi kasa shidai burin kyara da yake 

* Amma jama’a kusani sai munyi a sannu gudun kar muyi gaggawa 

Download Sai Muyi A Sannu Kada Muyi Gudun Gaggawa
Rarara ya zama zakaran dafi a wakokin siyasa Bayan Gwamnatin shugaba Buhari ta cika shekara 100 yayi wakar data ratsa zuciyar mai sauraro wadda yasa ma suna BINCIKE MUKE wakar ta zama ta Farko a lokacin ganin irin sakonnin daya sa a wakar 

  Download BINCIKE MUKE music…     

Rarara baiyi sake ba ya cigaba daba shugaba Buhari gudummuwa sosai daga bangaren shi na Mawaki rarara yayi wa Buhari waka mai taken SAI BUHARI SAI BABA itama wakar Rarara yayi nazari sosai kafin yayi ta ganin yadda ya saki bayanai a wakar dama kanshi salon kidan 

Download SAI BUHARI SAI BABA music… 

Haka Rarara bai gajiya ba wurin taimakawa shugaba Buhari ta fannin yada Labarai Rarara ya fitar da wakar shi mai taken KAFISU GASKIYA BABA rarara bai Gaza ba ganin yadda salon wakar yake 

Download KAFISU GASKIYA BABA music… 

Allah ya kara ma wannan Hazikin Mawakin Basira wato Alh. Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, Allah ya tsare shi, Allah ya taimake shi a Duk lamuranshi

Rubutawa:- Uthman Kharouphy

Tacewa da yadawa:- Umar Ibraheem G-Star

Daukar Nauyi:- Yahaya Madawaki’Wazirin Rarara’

Leave A Reply

Your email address will not be published.